Home Labaru Zaben Gambia: Barrow Ya Kama Hanyar Tazarce A Shugabanci

Zaben Gambia: Barrow Ya Kama Hanyar Tazarce A Shugabanci

176
0
Shugaban Gambia mai ci Adama Barrow na kan gaba a samakon farko na wasu yankuna da aka fitar bayan zaben ranar Asabar dake matsayin zakaran gwajin dafi ga demokradiyar kasar bayan Yaya Jameh.

Shugaban Gambia mai ci Adama Barrow na kan gaba a samakon farko na wasu yankuna da aka fitar bayan zaben ranar Asabar dake matsayin zakaran gwajin dafi ga demokradiyar kasar bayan Yaya Jameh.

Barrow wanda ya kawo karshen mulkin Yahya Jammeh na shekaru 22, yanzu haka ya kama hanyar tazarce a wa’adi na biyu, bayan da sakamakon farko na hukumar zaben kasar ya nuna shi ke kan gaban babban abokin hamayyar sa Ousainou Darboe  a kusan gundumomi 40, daga cikin 53 na fadin kasar.

Wani jami’in hukumar zaben ya shaidawa manema labarai a Banjul babban birnin kasar cewa ya kamata a bayyana sakamakon karshe da yammacin Lahadin nan.

Leave a Reply