Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya ba magoya bayan jam’iyyar tabbacin nasara a zaben gwamnan Edo mai zuwa.
Oshiomhole, ya sha alwashin tsige Gwamna Godwin Obaseki daga kujerar sa na zaben Satumba.
Da yake jawabi ga magoya bayansa a Edo a karshen mako, ya nuna karfin gwiwar cewa APC za ta yi nasara a zaben ranar 19 ga watan Satumba.
Da yake hannunka mai sanda ga Godwin Obaseki, gwamnan jihar mai ci, Oshiomhole ya ce ya yi farin ciki da cewar “Allah ya fitar da maciji daga cikin su.
Oshiomhole, wanda ya yi tsit tun bayan da kwamitin masu ruwa da tsaki ya rushe shugabancin jam’iyyar, ya ce ya dawo kan kafafunsa domin kwato jihar.