Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta yi watsi da bukatar jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar, ta neman a soke wata bukata da jam’iyyar APC ta gabatar a gaban ta.
A hukuncin da ya samu sahalewar alkalan kotun biyar, kotun ta ce bukatar ta Atiku da PDP su ka gabatar ba ta da sahihanci, don haka ta yi watsi da ita.
Idan dai ba a manta ba, a ranar 14 ga watan Mayu ne jam’iyyar APC ta nemi kotun ta yi watsi da jerin wasu jihohi 10 da jam’iyyar PDP ta gabatar a gaban kotu, bisa zargin cewa an tafka magudi tare da saba ka’idojin zabe a jihohin, bukatar da jam’iyyar PDP ta kalubalanta.
Jam’iyyar APC, ta kara neman kotun ta cire sunan mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da Janar Tukur Buratai da sauran shugabannin hukumomin tsaro, wadanda PDP ta hada da su a cikin takardar shigar da kara, bisa zargin su da hannu a magudin zaben da su ka zargi APC da tafkawa. Sai dai jam’iyyar APC ta hannun lauyan ta Lateef Fagbemi, ta janye wannan bukata a ranar 15 ga watan Mayu tare da sake mika wata sabuwar bukatar, lamarin da ya sa Atiku da PDP su ka daukaka kara zuwa kotun koli.