Home Labaru Zaben Bayelsa: PDP Ta Lashe Dukkan Kujerun Kananan Hukumomi 8

Zaben Bayelsa: PDP Ta Lashe Dukkan Kujerun Kananan Hukumomi 8

393
0

Jam’iyyar PDP a jihar Bayelsa, ta lashe dukkan kujerun kananan hukumomi takwas da na kansiloli a zaben kananan hukumomin da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Rahotsnni sun ce, masu zabe ba su fita rumfunan zabe yadda ya kamata ba, duk kuwa da cewa an gudanar da zaben a cikin kwanciyar hankali.

Shugaban hukumar zabe na jihar Bayelsa Dr. Remember Ogbe ya shaida wa manema labarai cewa, an gudanar da zaben ne a kananan hukumomi takwas cikin lumana, kuma irin sa na farko a tarihin jihar.

Ya ce duk zaben da ya samu kashi 60 cikin 100 na fitar masu zabe, wannan abin godiya ne ga Allah kasancewar an kammala shi cikin kwanciyar hankali.

Dr Ogbe ya kara da cewa, jam’iyyu 44 daga cikin 91 ne su ka shiga zaben, amma jam’iyyar APC na daga cikin jam’iyyun da ba su shiga zaben ba.

Leave a Reply