Home Labaru Zaben Bauchi: APC Ta Shigar Da Kara Kotu, Lauyoyi 50 Za Su...

Zaben Bauchi: APC Ta Shigar Da Kara Kotu, Lauyoyi 50 Za Su Kare PDP Kyauta

310
0

Biyo bayan kudirin gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar na kalubalantar nasarar Sanata Bala Mohammed, wasu lauyoyi sun ce a shirye su ke su tura lauyoyin 50 domin kare zababben gwamnan da kuma jam’iyyar PDP a gaban kotu.

Kungiyar ta yi nuni da cewa, yunkurin da APC da gwamnan jihar Bauchi su ka yi na shigar da kara kotu bayan shan kaye a zaben tamkar yin amai da lashewa ne, domin tuni gwamnan ya amince da shan kaye ya kuma taya zababben gwamna murna bayan sanar da sakamakon zaben.

Lauyoyin sun kara da cewa, a matsayin su na lauyoyi ba su da wata matsala da gwamna Mohammed Abubakar da jam’iyyar APC na zuwan su kotu domin kalubalantar nasarar Sanata Bala Mohammed.

Sun ce wannan ma yunkuri ne mai kyau, domin hakan zai ba su damar yin amfani da baiwar da Allah ya ba su wajen kare zabin al’umma wato Sanata Bala Mohammed.

Kungiyar lauyoyin ta kara da cewa, a kan haka, su na tabbatar wa zababben gwamnan da daukacin al’umar jihar Bauchi cewa za su tura akalla lauyoyi 50 da su ka hada da manyan lauyoyi domin kare zabin al’umma.

Leave a Reply