Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Zaben Amurka: Trump Ya Bukaci Masu Zabe Su Kada Kuri’a Sau Biyu

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci masu zabe a jihar North Carolina da su kada kuri’a sau biyu yayin zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.

Shugaba Trump ya bayan bukatar hakan ne yayin wata ziyara da ya kai jihar, inda ya ce bai gamsu da yadda yawancin al’ummar jihar suka amince su yi zabe ta hanyar aika kuri’unsu ta akwatun gidan waya ba.

A don haka ne ya bukaci masu zabe a jihar su kada kuri’a a ta hanyar da aka saba wato bin layin jefa kuri’a, ko da kuwa sun aika kuri’unsu ta akwatun aikawa da sakonnin gidan waya.

Trump na zargin aika kuri’a ta gidan waya na iya taimakawa abokin hamayyarsa Joe Biden.

A baya dai shugaban ya sha yin zargin cewa yin zabe ta akwatun gidan waya na iya haifar da magudi.

Masu suka na zargin shugaban kasar da kokarin kawo nakasu ga kwarin gwiwar da jama’a ke da shi a kan zaben.

Shugaba Trump da kwamitin yakin neman zabensa na ta hankoron ganin sun samu karbuwa a muhimman jihohin kasar da ke bawa dan takara damar lashe zaben shugaban kasa idan ya samu mafi rinjayen kuri’unsu.

Exit mobile version