Home Labaru Zaben 2023: Ya Kamata Mulki Ya Koma Kudu — Malam Ibrahim Shekarau

Zaben 2023: Ya Kamata Mulki Ya Koma Kudu — Malam Ibrahim Shekarau

341
0

Dan majalisar dattawan mai wakiltan Kano ta tsakiya a majalisar
dattawa, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce shugaban kasa na gaba
ya zo daga kudanci domin nuna adalci.

Malam Ibrahim Shekarau, ya ce duk da cewa ba ya rubuce a
kundin tsarin mulkin, akwai fahimtar daidaito da kuma ba kowa
daman kama ludayin domin adalci.

Ya ce ya kamata ayi da kowa, duk da cewar “kundin tsarin
mulkin Najeriya ko na jam’iyyar bai ce idan ni dan Arewa ne,
wajibi ne mataimaki na ya zo daga kudu ba.

Malam Ibrahim Shekarau, ya ce Arewa ta yi shugabancin kasa
na shekaru 8, amma aikin hankali shi ne a duba dayan bangaren,
ya koma kudancin Najeriya.

Leave a Reply