Home Home Zaben 2023: Wasu ‘Yan Siyasa Na Dumama Yanayi Da Zafafan Laffuza -Kwararru

Zaben 2023: Wasu ‘Yan Siyasa Na Dumama Yanayi Da Zafafan Laffuza -Kwararru

196
0

Kwamitin wanzar da zaman lafiya a jihar Kano ya ce yana aikin tsara wani taron masu ruwa da tsaki da shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa Janar Abdussalami Abubakar zai jagoranta a Kano.


 Sai dai kwamitin ya gargadi shugabanin Jam’iyyun siyasa da ‘yan takara a matakai daban daban su kiyaye laffuzan su yayin tarukan neman kuri’ar Jama’a.
Comrade Ibrahim Abdullahi Wayya dake kula da ayyukan sakatariyar kwamitin yace, shugabancin kwamitin ya bukaci hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki su tashi tsaye sosai.


Ya kara da cewar Kalmar tsiya-tsiya da shugaban Jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas yayi amfani da ita a yayin taron su na kamfe da kuma martanin makamanciyar wannan kalma da shugaban NNPP na Umar Haruna Doguwa ya furta a makon jiya, na daga cikin laffuzan da suka daga hankalin wannan kwamiti, domin kuwa kalamai ne da ka iya tada fitina a tsakanin al’uma ne 
Tuni dai masu kula da lamura ke da ra’ayin cewa, gargadin da kwamitin zaman lafiyar na Kano a wannan gaba, tamkar fargar jaji ne, la’akari da yadda wadancan lafuza suka fara mummunan tasiri. 

Leave a Reply