Home Labarai Zaben 2023: Takarar Musulmi Da Musulmi Ba Aibu Bane A Dumokaradiyya

Zaben 2023: Takarar Musulmi Da Musulmi Ba Aibu Bane A Dumokaradiyya

231
0


Shugaban  Kungiyar Tinubu Support Group Dr. Nasir Ladan Argungun ya bayyan cewar ya bukaci yan Najeriya da su yi la’akari da cancanta a zaben shugaban kasa na shakara ta 2023 ba wai cece kuce kan takarar musumli da musulmi ba.

 Dr. Nasir Ladan Argungun ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin Labarai na Najeriya wata NAN a Abuja, a yayin da kungiyar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar  APC suka kai masa ziyarar ban girma gabannin shirye-shiryen kaddamar da kwamitin yakin neman zabe na Dantakarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Sanata Bola Ahmed Tinubu,

Dr. Nasir ya ce ya kamata yan Najeriya  su yi la’akari da irin ayyukan cigaban da Sanata Bola Tinubu ya yi a lokacin yana Gwamnan jihar Legas duk da Gwamnatin Olushegun Obasanjo ta dakatar da baiwa jihar kudin kasafi na illahirin kanannan hukumomin jihar,

 Ya kara da cewar halin kalubalen tsaron da Najeriya take ciki na garkuwa da  jama’a don neman kudin fansa, da fashi da makami na cigaba da ta’azzara ne a sanadiyyar tabarbarewar tattalin arzikin kasa, inda jaddada cewar matukar Bola Tinubu ya samu nasarar darewar karagar shugabancin kasar nan zai yi amfani da hazakarsa wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Leave a Reply