Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP Sanata Walid Jibrin, ya ce nan bada dadewa ba za su fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin zakulo wan da zai daga tutar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na shekara ta 2023.
Walid ya bayyana haka ne, yayin da ya ke ganawa da manema labarai a Kaduna, inda ya ce duk wani dan jam’iyya da ke da ra’ayi ya na da ‘yancin tsayawa takara.
Sanata Wali ya kara da cewa, Atiku Abubakar ya na da damar tsayawa kamar kowane dan jam’iyyar matukar ya na da burin yin hakan.
Ya
ce shugabannin jam’iyyar PDP tare da hadin gwiwar sauran bangarorin ta za su
bayyana shirin da su ke yi na zaben dan takarar shugaban kasa a shekara ta 2023.