Home Labaru Zaben 2023: Nuna Isa Da Murza Gashin Baki Ba Zai Ba Mu...

Zaben 2023: Nuna Isa Da Murza Gashin Baki Ba Zai Ba Mu Shugabanci — Anyim

308
0

Tsohon Shugaban majalisar Dattawa Pius Anyim Pius, ya bayyana wasu matakai da idan ‘yan kabilar Igbo su ka yi amfani da su za su iya kaiwa ga samun kujerar shugabancin Nijeriya.

Pius Anyim ya bayyana haka ne, a wani taron ‘yan Kabilar Igbo da aka yi a jihar Abia, inda ya ce abubuwa biyu da Inyamirai za su yi su iya kaiwa ga yin nasarar darewa shugabancin Nijeriya a 2023 su ne, idan su ka kwantar da hankalin su su ka daina ganin su kadai ne shafaffu da mai a kasar nan su na raina wasu.

Ya ce Inyamurai su na raina abokan zaman su ta hanyar nuna su ba kowan-kowa ba ne su ne su ka isa, ya na mai cewa yin hakan ba zai kai su ga samun shugabancin Nijeriya ba.

Anyim ya kara da cewa, yanzu dai ya nuna kakara cewa yankin su ya na bukatar zama shugaban kasa, amma samun hakan ba zai yi wu ba idan su ka ce za su rika fankama su na nuna ‘yan wasu yankin ba su isa ba.