Home Labarai Zaben 2023 Ne Mafi Karancin Tashin Hankali a Tarihin Najeriya – Gwamnati

Zaben 2023 Ne Mafi Karancin Tashin Hankali a Tarihin Najeriya – Gwamnati

3
0

Gwamnatin tarayya ta yi ikirarin cewa, zaben shekara ta 2023
da ya gudana shi ne mafi karancin tashin hankali da aka taba
gani a tarihin Nijeriya.

Ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed, ya ce zaben bana shi ne wanda aka taba gani ba tare da tsananin tashe- tashen hankula ba a tarihin Nijeriya.

Lai Mohammed dai ya na halartar wani taro a kan sha’anin tafiyar da mulki da nufin kawo karshen rikice-rikice a kasashe ta hanyar hada hannu da tawagar ‘yan jaridun kasa da kasa da cibiyoyin ilimi da koya dabarun siyasa a birnin New York.

A wata kebantacciyar tattaunawa tsakanin Lai Mohammed da jami’in cibiyar Hudson Institute da Atlantic Council da Wilson Institute, ministan ya ce duk da cewa an samu rahoton mutuwar mutane 13 zuwa 28 yayin zaben na shekara ta 2023, adadin ya zama mafi karanci da aka taba gani tun daga shekarun 1964 da 1965 da aka fara zabe lokacin da mutane fiye da 200 su ka mutu.

Ya ce ko a zaben shekara ta 1993 sai da mutane 100 su ka rasa rayukan su, yayin da a shekara ta 1999 wasu 80 su ka mutu, sannan sama da mutane 100 su ka mutu yayin zabe a shekara ta 2003, sai kuma wasu 200 a shekara ta 2007.