Home Labaru Zaben 2023: Matasan Arewa Sun Nesanta Boss Mustapha Da Takarar Tinubu

Zaben 2023: Matasan Arewa Sun Nesanta Boss Mustapha Da Takarar Tinubu

475
0
Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Tarayya
Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Tarayya

Hadakar kungiyar matasan arewa wato CONYA a takaice, ta yi watsi da rahotannin da ke danganta sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da tararar Bola Ahmed Tinubu na neman shugabancin Nijeriya a zaben shekara ta 2023.

Da ya ke jawabi a wajen wani taro da su ka gudanar, shugaban kungiyar na kasa Kwamred Nuhu Sani Lere, ya ce masu baza wannan jita-jitar su na yi ne kawai don kashin kan su, ya na mai cewa babu abin da ke gaban Boss Musatapaha a matsayin sakataren gwamnatin tarayya da wuce sauke nauyin da shugaba Muhammadu Buhari ya dora ma shi domin fita hakkin ‘yan Nijeriya.

Nuhu Sani Lere ya kara da cewa, masu alakanta takarar Tinubu da Boss Mustapha su na yi ne domin haddasa rudani a zukatan ‘yan Nijeriya, amma babu abin da Boss Mustapha ya sa a gaba illa sauke nauyin da ya rataya wuyan sa don ganin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ba marada kunya.

A karshe ya bayyana Boss Mustapha a matsayin mutum mai dottako, kuma ba ya da alaka da duk wani labari na fitowa takara a zaben shekara ta 2023.

Leave a Reply