Home Home Zaben 2023: Ku Zabi ’Yan Takarar PDP, Amma Banda Na Shugaban Kasa- Nyeson

Zaben 2023: Ku Zabi ’Yan Takarar PDP, Amma Banda Na Shugaban Kasa- Nyeson

34
0

Gwamna Nyesom Wike ya bukaci al’ummar Jihar Ribas  su zabi jam’iyyar PDP a kowane mataki amma ban da kujerar shugaban kasa a babban zabe mai zuwa.

Wike ya kuma bukaci al’ummar jihar da su ba shi lokaci har ya kai ga bayyana musu mutumin da za su zaba a kujerar shugaban kasa.

Ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da wani aikin titi a yankin  karamar hukumar Obio/Akpor ta jihar.

 Ya ce  ku zabi dan takarar mu na gwamna, ku zabi ‘yan takararmu na majalisar wakilai, ku zabi ‘yan takararmu na Sanata, ku zabi ‘yan takarar mu na majalisa.

Gwamna Nyesom Wike ya kara da cewar duk wadanda muka ambata, ku tabbatar kun zabe su, shi kuwa da yan dan takarar shugaban kasa, nan ba da jimawa ba za mu hadu a gidajen mu, don yanke shawarar wanda za mu zaba.

Bayanai sun ce Wike da wasu gwamnoni hudu na jam’iyyar PDP da ake kira G5 sun shiga takun-saka da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar da kuma shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu.