Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-rufa’i, ya nemi a miƙa wa yankin kudu mulki a shekarar 2023 bayan wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ya kare.
Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai, ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da kafar BBC.
Ya ce idan aka lura ba ya ɗaukar mutum aiki domin shiyyar da ya fito, cancanta yake dubawa, yana duba wanda idan aka ba shi amanar jama’a zai riƙe ta yadda ya kamata ne.
Ya kuma ce, a siyasar da ake yi a Najeriya, akwai tsarin da ake bi na karba-karba, inda kowa ya amince cewa idan arewa ta yi mulki shekara takwas, kudu za ta yi mulki shekara takwas.
Ya ce duk da ba a rubuta tsarin karɓa-karɓan a tsarin mulki ba, amma kowane ɗan siyasa a ƙasa ya san da haka, shi yasa ya fito ya ce bayan shugaba Buhari, ya yi shekara takwas, ka da wani ɗan arewa ya nemi shugaban kasa, a bar ‘yan kudu suma su sami shekara takwas.
Da aka tambaye shi ko da gaske yana da ra’ayin tsayawa takarar shugabancin Najeriya, sai ya ce ana cewa yana son shugaban ƙasa tun yana ministan Abuja, amma ko kadan bai taba sha’awar shugabancin kasa ba.
You must log in to post a comment.