Home Labaru Zaben 2023: Dan Takarar Arewa Za Mu Mara Wa Baya – Kwande

Zaben 2023: Dan Takarar Arewa Za Mu Mara Wa Baya – Kwande

449
0

Mukaddashin shugaban kungiyar Dattawan Arewa Alhaji Musa Liman Kwande, ya ce al’ummomin yankin za su zabi mutumin Arewa ne ko a wace jam’iyya ya tsaya takara a zaben shekara ta 2023.

Musa Liman Kwande ya nuna cewa, babu ruwan sa da jam’iyya a zabe mai zuwa, ya na mai cewa wannan shi ne ra’ayin kashin kan sa a matsayin shi na dan kasa kuma mutumin Arewa.

Yayin da ya ke jawabi a birnin Lafia na jihar Nasarawa, Liman Kwande ya ce ba ya na magana ne a madadin kungiyar sa ba.

Kwande ya shaida wa manema labarai cewa, kungiyar tuntuba ta al’ummomin Arewa da Takwarorin ta ta, su na kokarin kawo wa yankin Arewa da Nijeriya cigaba ne kamar sauran kungiyoyi da su ka hada da ta Afenifere da Ohaneze a Kudacin Nijeriya.

A karshe ya bukaci daukacin mutanen Arewa su rika zaben ‘yan siyasa masu kishi da kuma nufin ci-gaba.