Home Labaru Zaben 2023: Babu Kowa A Zuciya Ta Da Zai Gaje Ni –...

Zaben 2023: Babu Kowa A Zuciya Ta Da Zai Gaje Ni – El-Rufai

639
0
Gwamnatin Kaduna ta ba jami'an tsaro umurnin daukar mataki kan masu karya dokar hana fita saboda coronavirus
Jihar Kaduna ta nuna bacin rai bisa yadda jama'a ke karya dokar hana fita.

Gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna, ya musanta rahotannin da ke cewa ya zabi wanda zai maye gurbin shi a shekara ta 2023.

El-Rufa’i ya sanar da haka ne, yayin da wasu mutane ke tunanin cewa namiji ne zai maye gurbin sa da wata mace a matsayin mataimakiya kamar yadda ya yi da Hadiza Balarabe.

Ya ce kamar yadda ya sani, ya yi wuri a fara maganar zaben shekara ta 2023, domin Ubangiji ne kadai ya san wanda zai maye gurbin shi a matsayin gwamnan jihar Kaduna.

El-Ruufa’i, ya ce ya ji abubuwa da yawa da mutane ke cewa a kan wanda zai gaje shi, sai dai ya ce ba ya da kowa a zuciya da ya ke tunanin zai maye gurbin shi. Ya ce a bar talakawa su zabi shugaban su da kan su, ya na mai cewa, Ubangiji ne kadai zai iya zaben shugaba na gaba, ya na mai cewa fatan shi kawai shi ne, Allah ya zabi mafi alkhairi da zai kai jihar Kaduna gaba.