Home Labaru Zaben 2023: Arewa Ba Za Ta Lamunci Tsarin Karba-Karba Ba – Ango

Zaben 2023: Arewa Ba Za Ta Lamunci Tsarin Karba-Karba Ba – Ango

724
0
Farfesa Ango Abdullahi, Babban Jigo A Kungiyar Dattawan Arewa
Farfesa Ango Abdullahi, Babban Jigo A Kungiyar Dattawan Arewa

Shugaban kungiyar dattawan arewa Farfesa Ango Abdullahi, ya ce yankin arewa na iya ci-gaba da rike mulkin Nijeriya har nan da tsawon shekaru 100 idan ta na so, domin damokradiyya na kunshe ne da adadi da kuma yankin da ke da karfin cimma hakan.

Ango Abdullahi ya bayyana haka ne, yayin da yake magana a kan sanin rabe-raben wa’adin shugabanci, a daidai lokacin da ake tsinkayar zaben shekara ta 2023.

Farfesan ya bayyana wa manema labarai cewa, arewa za ta mara wa ‘yan takara daga yankin baya ne kawai a zaben shekara ta 2023. Ya ce rabe-raben shugabancin karba-karba da mafi akasarin shugabannin kudu ke fafutuka akai ya saba wa kundin tsarin mulki, kuma shugabannin arewa ba za su goyi bayan haka ba.