Home Labarai Zaben 2023: Ana Nuna Fargaba Kan Yadda Masu Zabe Ke Saida ‘Yancinsu...

Zaben 2023: Ana Nuna Fargaba Kan Yadda Masu Zabe Ke Saida ‘Yancinsu A Nijeriya

142
0

Masu sharhi a kan harkoki siyasa a Nijeriya, sun fara nuna fargabar cewa akwai yiwuwar wasu masu hannu-da-shuni da ke neman wani mukami a zaben shekara ta 2023 za su yi amfani da kudi wajen sayen kuri’un mutane domin cimma burin su.

An dai soma fargabar ne bayan wani bidiyo da aka dauka a wajen zaben gwamnan jihar Ekiti a baya-bayan nan, inda aka nuna wasu ‘yan siyasa su na raba wa masu kada kuri’a kudade.

Haka kuma, a zabubbukan fidda gwani da aka kammala an ga tasirin hakan, inda aka ga wani daliget ya na raba wa ‘yan mazabar sa kudin da ya ce wani dan takarar shugaban kasa ne ya ba shi.

Shugaban Cibiyar tabbatar da ci-gaba da dimokradiyya kuma mai sharhi a kan harkokin siyasa Dakta Kole Shettima, ya ce wannan abu da ‘yan siyasa ke yi ya na da matukar illa.

Ya ce idan ba a yi sa’a ba, a zabubbuka masu zuwa sai mai kudi ne zai samu nasara ko da bai cancanta ba, ya na mai cewa, bisa la’akari da halin da ake ciki na talauci da tsadar kayayyaki a Nijeriya, masu neman mukaman siyasa za su iya amfani da yanayin da mutane ke ciki su ba su kudi domin su zabe su.

Leave a Reply