Home Labaru Zaben 2019: Shahadun Cin Zabe Na Mutane 70 Hukumar Zabe Ta Kwace...

Zaben 2019: Shahadun Cin Zabe Na Mutane 70 Hukumar Zabe Ta Kwace – Okoye

316
0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa INEC, ta ce ta janye shahadun nasarar lashe zabe na mutane 70 da aka bada bayan zaben shekara ta 2019.

Kwamishinan Wayar da Kan jama’a a kan harkokin zabe na Kasa Festus Okoye ya bayyana haka, a wajen wani taron da Gidauniyar Kofi Annan ta shirya a Abuja.

Okoye ya kara da cewa, daya daga cikin manyan kalubalen da hukumar ke fuskanta sun hada da rigingimun zaben fidda-gwani da ke gaban kotuna tun kafin a yi zaben shekara ta 2019.

Ya ce ya zuwa yanzu hukumar ta na da kararraki 809, wadanda ke kotu tun kafin a yi zaben shekara ta 2019, sai kuma wasu 800 da aka kai kotuna bayan zaben.

Festus Okoye, ya ce an kwace shahadun mutanen ne bayan kotu ta yanke hukuncin cewa ba su ne halastattun ‘yan takara ba, kuma tuni hukumar ta sake buga wasu takardun ta ba wadanda kotu ta ce su ne halastattu.