Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Zaben 2019: Kungiyar Tarayyar Turai Ta Gabatar Rahoto Ga INEC

Tawagar kungiyar tarayyar turai da ta sanya ido kan harkokin zaben shekarar 2019, ta mika rahoto kan wuraren da take ganin an samu kura-kurai a zabubbukan da suka gabata.
A lokacin da yake gabatar da rahoton ga shugaban hukumar zabe Mahmud Yakubu a Abuja, jagoran tawagar Maria Arena, ta ce a yau kungiyar za ta bayyana rahoto kan zaben.
Arena ta ce za a bayyana dukkanin abubuwan dake cikin rahoton da suka gabatar ga ‘yan jaridu da kuma sauran ‘yan kasa baki daya, kamar yadda kungiyar ta alkawarta a baya.
The EU chief observer said that the union had been part of Nigeria’s electoral process since 1999.
Kungiyar dai ta tura da wakilanta 73 a rumfunan zabe 223 da kuma cibiyoyin tattara sakamakon zabe a jihohi 22 lokacin zaben shekara ta 2019.
A lokacin da yake karbar rahoton, shugaban hukumar zaben Mahmud Yakubu, ya ce kungiyar tarayyar turai, ta dade tana taimakawa wajen ganin an samu daurewar demokradiyya tun a shekarar 1999.
Sannan ya ce hukumar za ta yi aiki da shawarwarin da hukumar ta gabatar a zabubbukan da za ta gudanar nan gaba.

Exit mobile version