Home Labaru Zaben 2019: Kungiyar EU Ta Gabatarwa INEC Rahoto Kan Zaben

Zaben 2019: Kungiyar EU Ta Gabatarwa INEC Rahoto Kan Zaben

326
0

Kungiyar kasashen tarayyar turai ta gabatar da rahoton ta kan zaben 2019 ga Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, inda hukumar ta yi alkawarin yin bita kan rahoton.
A lokacin da ta ke gabatar da rahoton ga shugaban hukumar zabe, Farfesa Mahmood Yakubu, shugabar tawagar, Maria Arena ta ce za su wallafa rahoton domin al’umma su karanta
Shugabar kungiyar ta ce, kungiyar ta kasance ta na bibiyar zabukan Najeriya tun a shekara ta 1999, kuma a yanzun kungiyar ta samar da masu sa ido kan zabe guda 73 da aka baza a rumfunan zabe 223 da dakin kidayan kuri’u 81 a jihohi 22 a lokacin zaben 2019.
Arena, ta ce nan ba da dadewa ba za ta ba ‘yan jarida da sauran al’umma rahoton domin su nemi karin bayani kan wasu batutuwa da aka tattauna akai.
Shi kuwa shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya amince da cewa kungiyar EU ta kasance abokiyar huldar Najeriya wajen wanzar da ci gaban demokradiyya tun 1999.
Yakubu, ya ce hukumarsa ta kaddamar da shawarwarin da EU ta bayar a zabukan da suka gabata, shawarwarin sun hada da tantance masu zabe da jefa kuri’a a lokaci guda da aka fara amfani da shi a zaben gwamnan jihar Bayelsa a 2015 bayan an kammala sauran.

Leave a Reply