Home Labaru Zaben 2019: Jam’iyyu 75 Sun Yaba Wa Shugaban Hukumar Zabe

Zaben 2019: Jam’iyyu 75 Sun Yaba Wa Shugaban Hukumar Zabe

198
0

Jam’iyyun siyasa 75 sun jinjina wa kokarin Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa Farfesa Mahmood Yakubu.

A cikin wani jawabin bayan taro da su ka fitar a Abuja, jam’iyyun sun amince tare da gamsuwa da cewa Yakubu da hukumar zabe sun taka rawar gani matuka wajen gudanar da zaben shekara ta 2019.

Jam’iyyun sun amince da cewa, yawancin matsalolin da aka fuskanta duk ba laifin hukumar zaben ba ne.

A karshe sun yi kira ga Majalisar Tarayya ta sake gaggauta aika wa Shugaba Mujammadu Buhari Kudirin Gyaran Dokokin Zabe domin a tabbatar da an maida su doka.