Jam’iyyar PDP ta jinjina wa Wakilan Sa-ido na Tarayyar Turai, game da rahoton da su ka fitar dangane da yadda zaben shekara ta 2019 ya gudana a fadin Nijeriya.
Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar PDP ya yi wannan jinjina a cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya fitar a Abuja.
Olagbondiyan, ya ce abubuwan da rahoton ya fallasa ya kara tabbatar da zarge-zargen da jam’iyyar PDP da milyoyin ‘yan Nijeriya su ka yi a kan yadda zaben ya gudana.
Ya ce yanzu duniya za ta tabbatar da cewa, ba wai a banza PDP ta rika kukan an yi mata magudi ta hanyar rage mata kuri’u ba.
Ya ce rahoton ya fallasa yadda aka yi harkallar akwatunan zabe, da yadda kayan zabe su ka yi layar-zana da yadda aka rika kin yi wa mai jefa kuri’a alamar ya jefa kuri’a.