Home Labaru Zaben 2019: Hukumar Zabe Ta Bukaci Kotu Ta Yi Watsi Da Karar...

Zaben 2019: Hukumar Zabe Ta Bukaci Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Atiku Da PDP

417
0

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta bukaci kotun sauraren kararrakin zabe ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar su ka shigar a kan nasarar shugaba Muhammadu Buhari.

Jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar dai su na kalubalantar nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben shekara ta 2019.

A wata bukata da hukumar zaben ta shigar ta bakin lauyan ta Hustaz Usman, ta bukaci kotun ta yi fatali da bukatar PDP a kan rashin ambatar sunan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a cikin karar da ta shigar.

Lauya Hustaz Usman ya kuma shigar da wasu bukatu hudu daban-daban domin kokarin gamsar da kotun a kan watsi da korafin PDP, lauyan PDP Levi Uzoukwu, ya siffanta bukatar a matsayin wani bakon abu a hakkokin kotu, kuma ya bukaci kotun ta yi watsi da wannan bukata.

Bayan sauraren shari’ar, shugaban kotun mai shari’a Mohammed Garba ya dakatar da zaman zuwa wani lokaci.

Leave a Reply