Home Labaru Zaben 2019: Buhari Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki A Karo Na Biyu

Zaben 2019: Buhari Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki A Karo Na Biyu

322
0
Muhammadu Buhari, Shugaban Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Nijeriya a karo na biyu.

Buhari ya isa dandalin Eagle Square da ke Abuja, inda za a rantsar da shi tare da Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo a karo na biyu.

Tsohon Shugaban kasa a Janar Yakubu Gowon da tsohon Shugaban kasa Cif Ernest Shonekan na daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron kaddamar da shugaban kasa Buhari ya karo na biyu da ya gudana a dandalin  Eagle Square da ke Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, tsoffin Shugabannin Nijeriya Olusegun Obasanjo da Ibrahim Badamasi Babangida ba su hallarci taron ba.

Sauran manyan mutanen da suka hallarci taron sun hada da ‘ya’yan kungiyar sojojin diflomasiyya da manyan ‘yan kasuwa irin su Aliko Dangote da gwamnoni da jiga-jigan jam’iyyar APC da yan majalisa tarayya da dai sauran su.

Leave a Reply