Home Labaru Zaben 2019: Atiku Abubakar Na Shirin Maka Shugaban Hukumar Zabe Kotu

Zaben 2019: Atiku Abubakar Na Shirin Maka Shugaban Hukumar Zabe Kotu

254
0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya fara tunanin maka shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu kotu bisa laifin saba wa hukuma.

Atiku Abubakar ya soma barazanar shigar da Mahmood Yakubu kotu ne saboda saba wa umarnin da kotu na cewa a mika wa Lauyoyin sa kayan da aka yi amfani da su a zaben da ya gabata.

Idan dai za a iya tunawa, kotun daukaka kara ta ba hukumar zabe umarnin fito da kayan zaben shekara ta 2019, domin Lauyoyin Atiku su gabatar da bincike game da shari’ar da ake yi.

Sai dai har yanzu hukumar zabe ba ta bi umarnin kotun ba, lamarin da ya sa Atiku ya ke tunanin kai shugaban hukumar zaben kara a kotu.

Lauyoyin Atiku sun ce a yanzu babu abin da za su iya, illa su shigar da karar Farfesa Mamood Yakubu laifin tubure wa umurnin kotu, inda za su nemi hukuma ta daure shi a gidan yari.

Daya daga cikin manyan Lauyoyin Atiku Abubakar Mike Ozekhome, ya ce Farfesa Mahmood Yakubu ya koma yi wa dokar kasa da umarnin kotu karan-tsaye, don haka dole su nemi a daure sa.

Leave a Reply