Home Labaru Zaben 2019: An Cigaba Da Zaman Sauraren Karar Da Atiku Da PDP...

Zaben 2019: An Cigaba Da Zaman Sauraren Karar Da Atiku Da PDP Su Ka Shigar

350
0
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta cigaba da sauraren karar da Atiku Abubakar ya shigar domin kalubalantar nasarar da shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya yi a zaben shekara ta 2019.

Tsohon shugaban hukumar EFCC Malam Nuhu Ribadu ne ya ke wakiltar shugaba Buhari a zaman kotun, yayin da shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus ya ke wakiltar Atiku Abubakar.

Jim kadan bayan zaman kotun na ranar Larabar nan, jam’iyyar PDP ta bukaci ganin shugabar tawagar alkalan kotun da ragowar mukarraban ta a dakin ganawa tare da Manyan lauyoyi biyu daga kowane bangare.An dai tsaurara matakan tsaro a harabar kotun da kewaye, domin nesanta wasu magoya bayan jam’iyyar PDP daga harabar kotun bisa zargin za su gudanar da zanga-zanga.

Leave a Reply