Gwamnatin Tarayya ta bayyana kwarin guiwar samun nasara a kotun sauraron karar zabe da za ta yanke hukunci kan karar kin amincewa da sakamakon da ya kawo Ahmed Bola Tinubu karagar mulki.
Baya ga sanarwa ta musamman daga kakakin shugaban Ajuri Ngelale na kwarin guiwar samun nasara, mai ba wa shugaban shawara na musamman kan harkokin siyasa Ibrahim Kabir ya ce ba sa shakka ko kokonton samun nasara.
Ita ma jam’iyyar APC ta bakin sakataren yada labaru Felix Morka ya ce Tinubu ya lashe zaben na 25 ga watan Febairu don haka su na da kwarin guiwar kotun za ta tabbatarwa Tinubu nasarar sa.
A Tatihin shari’un da a ka yi a baya tun fara wannan dimokradiyya a 1999 ba a taba soke zaben shugaban kasa a nada wani ko a sake zaben ba.
You must log in to post a comment.