Home Labaru Kasuwanci Za Mu Kai Ziyarar Ba-Zata Ga Bankunan Da Ake Zargi Da Cinikin...

Za Mu Kai Ziyarar Ba-Zata Ga Bankunan Da Ake Zargi Da Cinikin Dala Ta Haramtacciyar Hanya –CBN

35
0

Babban Bankin Nijeriya CBN, ya yi barazanar gurfanar da bankunan da su ke cinikayyar Dala ta haramtacciyar hanya.

Gwamnna riƙon ƙarya na bankin CBN Folashodun Shonubi, ya bayyana haka, yayin wata lacca da aka gabatar a kan samar da mafita ga tattalin arzikin Nijeriya a Abuja.

Taron dai ya mai da hankali ne a kan yadda za a katange shigar da kuɗaɗen gwamnati zuwa haramtacciyar hanya, tare da shigar da su inda ya dace domin kawo ci-gaban tattalin arzikin gwamnati.

Shonubi ya bada sanarwar cewa, zai haɗa kwamitin da zai fara kai ziyarar ba-zata zuwa bankunan da ake zargi da saida Dala ba bisa ƙa’ida ba, kuma duk banki da aka tabbatar ya na wannan harƙallar za a gurfanar da shi a gaban hukuma domin ladabtarwa.