Home Labaru Za A Hukunta Masu Hannu A Shigo Da Gurɓataccen Mai – Buhari

Za A Hukunta Masu Hannu A Shigo Da Gurɓataccen Mai – Buhari

104
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin cewa, duk masu hannu wajen sarrafawa da kuma shigo da gurɓataccen mai Nijeriya za su fuskanci hukunci daidai da abin da doka ta tanada kan su.

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce game da batun ƙarancin man fetur da ya faru sakamakon shigo da gurɓataccen mai, Shugaba Buhari ya ce kare lafiya da muradin al’umma ne mafi mahimmanci a gwamnatin sa, don haka za a ɗauki duk matakin da ya dace domin kare ‘yan Nijeriya daga illar amfani da gurɓatattun kaya kowane iri ne.

Garba Shehu, ya ce shugaban Ƙasa ya bada umarni cewa, a bi duk tsarin da doka ta tanada wajen gano asalin yadda lamarin ya faru, kuma duk wanda abin ya shafa ya na da haƙƙin ganin an saurari koken sa.