Hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta Nijeriya NiMET, ta yi hasashen cewa za a fuskanci yanayin hazo na tsawon kwanaki uku a faɗin Nijeriya daga ranar Alhamis zuwa Asabar.
Ta ce za a fi samun hazon ne a yankin arewacin Nijeriya, musamman a jihohin Yobe da Borno da Adamawa da kuma Taraba.
Hukumar ta kara da cewa, ƙura za ta mamaye yankin arewa ta tsakiya da biranen kudanci a tsawon wannan lokaci, ana kuma sa ran hazo da sanyi a biranen bakin teku a tsakanin wadannan ranaku.
Haka kuma, Hukumar ta shawarci mutanen da ke fama da matsalar numfashi su kare kan su, saboda yanayin kura da ake samu a yanzu ya na da haɗari ga lafiyar su.
You must log in to post a comment.