Home Labaru Kiwon Lafiya Za a Fuskanci Yanayin Hazo Na Kwana Uku a Najeriya – NiMET

Za a Fuskanci Yanayin Hazo Na Kwana Uku a Najeriya – NiMET

103
0

Hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta Nijeriya NiMET, ta yi hasashen cewa za a fuskanci yanayin hazo na tsawon kwanaki uku a faɗin Nijeriya daga ranar Alhamis zuwa Asabar.

Ta ce za a fi samun hazon ne a yankin arewacin Nijeriya, musamman a jihohin Yobe da Borno da Adamawa da kuma Taraba.

Hukumar ta kara da cewa, ƙura za ta mamaye yankin arewa ta tsakiya da biranen kudanci a tsawon wannan lokaci, ana kuma sa ran hazo da sanyi a biranen bakin teku a tsakanin wadannan ranaku.

Haka kuma, Hukumar ta shawarci mutanen da ke fama da matsalar numfashi su kare kan su, saboda yanayin kura da ake samu a yanzu ya na da haɗari ga lafiyar su.

Leave a Reply