Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani, ya ce gwamnatin shi za ta ƙaddamar da wani shirin buɗe wa mutanen karkara asusun ajiyar banki.
Uba Sani ya ce za a yi hakan ne domin taimaka wa mutane su samu tallafin da gwamnatin Tarayya ta ƙuduri aniyar aiwatarwa.
Ya ce binciken da su ka yi tare da Bankin Duniya, an gano cewa kashi 75 cikin ɗari na al’ummar arewa maso yamma ba su da asusun ajiya na Bankuna.
Uba Sani ya kara da cewa, idan kuma mutum ba ya da asusun ajiya a banki babu yadda za a yi tallafin ya same shi, kuma irin wannan ne ya sa akasarin tallafin da ake bayarwa a Nijeriya ya ke zuwa ga mutanen kudanci kawai.
Ya ce idan aka cigaba da yadda ake tafiya ba tare da an ɗauki mataki ba, al’ummar arewacin Nijeriya ba za su amfana da tallafin na gwamnatin tarayya ba.