Home Labarai Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kano: Kotu Ta Hana Jam’iyyun Siyasa 19 Kawo...

Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kano: Kotu Ta Hana Jam’iyyun Siyasa 19 Kawo Tangarɗa

49
0
Court and Law.webp
Court and Law.webp

Wata babbar kotun jihar Kano a ranar Talata, ta hana jam’iyyun siyasa 19 daukar duk wani mataki da zai kawo cikas ko Tangarɗa ga zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSIEC, ta hannun lauyanta Rilwanu Umar, ta shigar da karar ne mai kwanan wata, 20 ga watan satumba.

KANSIEC na neman kotu ta hana wadanda ake kara kawo cikas ga harkokin zabe a kananan hukumomi 44 da ke jihar,

wadanda ake kara kuma sun hada da jam’iyyar AP, da AA, da ADP, da ADC, da APC, da APM, da APGA, da BP da kuma LP.

Sauran sun hada da NRM, da NNPP, da PDP, da PRP, da SDP, da YPP, da YP da kuma ZLP.

Mai shari’a Sunusi Ado-Ma’aji, ya bayar da umarnin wucin gadi da ya hana wadanda ake kara yin duk wani mataki da zai hana KANSIEC gudanar da aikin ta wanda doka ta tanadar mata.

Ado-Ma’aji ya ɗage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 10 ga watan Oktoba, domin ci gaba da sauraron karar.

Leave a Reply