Hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta Najeriya wato INEC, ta ce akwai kimanin mutum miliyan biyu da dubu ɗari shida da aka tantance waɗanda za su jefa ƙuri’a a zaɓen da za a gudanar a jihar Edo ranar 21 ga wannan watan na Satumba.
Shugaban hukumar zaɓen, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da haka a Benin babban birnin jihar ta Edo.
Ya ce hukumar ta shirya tsaf domin fara jigilar muhimman kayayyakin zaɓen zuwa babban bankin Najeriya CBN nan da mako mai zuwa.
Za a fafata zaɓen ne tsakanin Sanata Monday Okpebholo na Jam’iyyar APC da Olumide Akpata na Jam’iyyar LP, waanda tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ne da kuma Asuerinme Ighodalo na Jam’iyyar PDP.