A yayin da jam`iyyun siyasa ke duba yankin da za su bai wa takarar shugabancin ƙasar nan, tuni wasu daga yankin arewa suka fara muhawara a kan wanda ya fi cancanta.
A zantawarsa da kafar yada labarai ta BBC wani jigo a jam’iyyar APC Abdurrahman Buba Kwacham, ya ce ganin matsalar da arewa ke ciki ya kamata abar mulkin a hannun Ɗan arewa.
Buba Kwacham ya ce, babu wanda zai tunkari matsalolin da yankin ke fama da su, da suka hada da satar mutane da rikicin Boko Haram, da koma-baya a fannin ilimi da sauran su kamar dan Arewa.
To sai dai wasu da daman a ganin cewa lokaci yayi da ya kamata mulki ya koma kudancin Najeriya a shekara ta 2023, tun da kudu ta ba arewa damar ci gaba a wa’adin mulki na biyu a shekarar 2019.
Shima wani jigo a Jam’iyar APC Dakta Dahiru Maishanu, ya ce lokaci ya yi da za’a nunawa kudancin Najeriyar hallaci.
Acewarsa ”A arewa shugaba Muhammad Buhari ya yi sau biyu, Obasanjo ya yi sau biyu, yanzu kuma lokaci ne da ya kamata a ba yankin kudu maso gabas ko kudu maso kudu.