Home Labaru Zaɓaɓɓun Gamayyar Jam’Iyyun Adawa Sun Kafa Kwamitin Fito Da Ɗan Takara Ɗaya...

Zaɓaɓɓun Gamayyar Jam’Iyyun Adawa Sun Kafa Kwamitin Fito Da Ɗan Takara Ɗaya Tilo 

114
0

Zaɓaɓɓun ‘yan majalisar wakilai daga jam’iyyun adawa
bakwai, sun ce za su yi amfani da yawan su a jimlace domin
su samar da shugabannin Majalisar Wakilai,

‘Yan majalisar dai sun hada da na Jam’iyyun PDP da Labour da NNPP da APGA da SDP da ADC da kuma YPP.

Zaɓaɓɓun ‘yan majalisar sun cimma matsayar ne a cikin wata sanarwa da Dachung Bagos na jam’iyyar PDP daga Jihar Filato da Afam Ogene na Labour daga Jihar Anambra da Gaza Gbefwe na SDP daga jihar Nassarawa, cewa za su cure wuri guda su 188 domin su kada duk wani ɗan takarar da APC za ta tsaida

Tuni dai sun kafa kwamitin mutane 13 a ƙarƙashin jagorancin Nicholas Mutu na jam’iyyar PDP daga jihar Delta.

Wani rikicin kuma ya ƙara kunno kai a cikin wakilan APC, inda manyan da ke sahun gaba a Majalisar kuma masu takarar shugabancin ta su ka ce ba su amince da wanda Bola Tinubu da APC ke so ya zama Kakakin Majalisar wakilan ba.

Leave a Reply