
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami’anta sun kama makudan daloli na jabu a Abuja.
Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce an yi yunƙurin sace kusan dala biliyan 2.7 na tattalin arzikin Najeriya ne ta hanyar tura kuɗaɗen na jabu a kasuwa da suka kai sama da dala miliyan 4.7.
Hukumar ta ce jami’anta sun kama kuɗaɗen da wanda ake zargi da ɗauko su ne daga Legas zuwa Abuja a yankin Abaji.
Shugaban hukumar ta NDLEA Birgediya Janar Buba Marwa ya bayar da umarnin a miƙa kuɗaɗen da wanda ake zargin ga hukumar EFCC domin ci gaba da bincike.













































