Home Home Yunkurin Gurfanar Da Aa Zaura A Kotu Ya Sake Gamuwa Da Cikas

Yunkurin Gurfanar Da Aa Zaura A Kotu Ya Sake Gamuwa Da Cikas

89
0
Yunkurin hukumar EFCC na gurfanar da ɗan takarar sanata na jam’iyyar APC a jihar Kano AbdulKareem AbdulSalam Zaura ya sake fuskantar cikas a kotu.

Yunkurin hukumar EFCC na gurfanar da ɗan takarar sanata na jam’iyyar APC a jihar Kano AbdulKareem AbdulSalam Zaura ya sake fuskantar cikas a kotu.

Babbar kotun tarayya da ke zama a Kano, ta ɗage gurfanar da A.A Zaura domin a ba sabon lauyan sa damar shirya tunkarar shari’ar.

EFCC dai ta na zargin AA Zaura ne da damfarar wani ɗan ƙasar Kuwait sama da dala miliyan daya, zargin da ya sha musantawa.

Duk da kasancewar EFCC ta sami nasarar kai shi gaban kotun, amma kotun ta ɗage zaman shari’ar saboda sabon sauyan sa Basil Hemba bai shirya ba, inda ya ce ya na buƙatar nazarin yadda zai tunkari batun kasancewar sa sabo a kan shari’ar.