Hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima wato NYSC ta karyata jita-jitar da ake yadawa a kafafen sadarwa na zamani cewa gwamnati ta karawa masu yi wa kasa hidima albashi daga naira 19 da dari 8 zuwa dubu 31 da dari 8.
Hukumar NYSC ta ce labarin bashi da tushe balle makama, idan akwai maganar karin kudin ita ya kamata ta sanar da jama’a ba wasu ba.
Mataimakin daraktan hukumar na kasa Eddy Megwa, ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce gwamnatin tarayya ba ta sanar da shirin karawa masu yi wa kasa hidima albashi ba.Ya kara da cewa, ko da yake ba hukumar ba ita ba ce ke biyan masu yi wa kasa hidima albashi ba, amma gwamnatin tarayya za ta sanar da hukumar idan akwai shirin karawa albashin.