Home Labarai Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza: Blinken Ya Sauka A Isra’ila

Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza: Blinken Ya Sauka A Isra’ila

38
0
3377
3377

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony ya sauka a  Isra’ila a wannan Lahadi a ƙoƙarin da ya ke na ci gaba da matsin lamba a game da tsagaita wuta a Gaza,

da kuma kauce wa bazuwar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya,

a yayin da wani babban jami’in Hamas ya yi watsi da abin da ya kira yin gaban kai da Amurka ta yi a tattaunawar Doha.

Blinken, wanda a karo na 9 kenan ya ke ziyartar Gabas ta Tsakiya tun da aka fara yaƙin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba, zai gana da jagororin Isra’ila kafin komawa tattaunawar da za a yi a birnin Alkahira.

Masu shiga tsakani daga Amurka, Masar da Qatar ssun ce an samun ci gaba a tattaunawar neman tsagaita wuta a yaƙin da aka shafe sama da watanni 10 ana yi,

kuma wani jami’in Amurka ya  ce ana yi cike giɓin da aka samu a yayin tattaunawar.

Amma wani  babban jami’in Hamas, Sami Abu Zuhri ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Faransa cewa batun ana daf da cimma yarjejenniya ‘almara’ ce.

A ranar Talata ake sa ran Blinken zai yi balaguro zuwa birnin Alkahira  na ƙasar Masar, inda za a koma tattaunawar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a cikin kwanaki masu zuwa.

Sai dai a yayin da ake ci gaba da matsa wa Isra’ila lamba a game da tsagaita  wuta, a wannan Lahadi, fira minista Benjamin Netanyahu ya jaddasa cewa ƙungiyar Hamas ta yankin Falaɗinawa ce ta kamata a matsa wa lamba.

Leave a Reply