Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yansanda Sun Kai Samame Gidan Matawalle, Sun Kwace Motoci 40

Gwamnatin Jihar Zamfara, ta bada umarnin kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle tare da kwace wasu motoci da ake kyautata zaton na gwamnatin jihar ne.

Idan dai za a iya tunawa, da ya ke magana a wani gidan rediyon yankin, Gwamna Dauda Lawal ya ce Matawalle ya tafi da motoci 17 daga ofishin sa da wadanda ke ofishin mataimakin gwamn sa, yana mai cewa motocina ne asali ma kayan ofis ma ba su tsira ba.

A ranar Asabar da ta gabata ne, Dauda Lawal ya ba Matawalle wa’adin kwanaki biyar ya maida motocin da ake zargin jami’an gwamnatin shi sun tafi da su.

Dauda Lawal ya bada wa’adin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Sulaiman Idris ya fitar, inda ya sha alwashin kwato kudade da kadarorin gwamnatin jihar Zamfara da aka sace.

Exit mobile version