Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International a Nijeriya, ta yi zargin cewa har yanzu jami’an tsaron Nijeriya su na gallaza wa jama’a tare da cin zarafin su ta hanyoyi daban-daban.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce da dama daga cikin irin mutanen da aka ci zarafin su ba su samun taimakon da ya dace, ko da kuwa sun kai kara wajen shugabannin jami’an tsaro da kuma kotuna.
Daraktan kungiyar a Nijeriya Osai Ojigho, ta ce duk da dokar Nijeriya ta haramta azabtar da mutane da kuma kafa kwamitin sake fasalin rundunar tsaro ta SARS, har yanzu ana samun wannan matsalar.
Kungiyar Amnesty dai ta jima ta na jefa ayar tambaya a kan gallazawar da jami’an tsaro ke yi wa jama’a a Nijeriya.
You must log in to post a comment.