Uwargidan Shugaban kasa A’isha Buhari, ta ce za ta jagoranci sauran matan gwamnoni wajen yaki da cin zarafin mata da kananan yara a arewacin Nijeriya.
A wasu sakonni da ta wallafa a shafin ta na Twitter, A’isha Buhari yi kira ga maza da mata da kananan yara su yaki duk wani nau’i na cin zarafi.
A’isha Buhari, ta kuma wallafa wani bidiyo a Twiiter, wanda ke nuna matan gwamnonin arewa su na bada bayanai a kan cin zarafin mata da kuma zaburar da mutane a kan su guji cin zarafin mata.
You must log in to post a comment.