Home Labaru ‘Yanci: Mun Amince Da Umarnin Buhari Na Sakar Ma Kananan Hukumomi Mara...

‘Yanci: Mun Amince Da Umarnin Buhari Na Sakar Ma Kananan Hukumomi Mara – Gwamnoni

371
0

Daukacin gwamnonin Nijeriya, sun bayyana amincewar su da tsarin sakar ma kananan hukumomi da bangaren shari’a kudaden su kai tsaye ba tare da sun bi ta hannun su ba kamar yadda shugaba Muhammadu Buhari ya bukata.

Shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya bayyana haka, a wajen taron kara wa juna sani a kan aiwatar da tsarin a Transcorp Hotel da ke Abuja.

Idan dai ba a manta ba, a shekarar da ta gabata ne shugaba Buhari ya sa hannu a kan dokar ‘yantar da kananan hukumomi da bangaren shari’a matakin jahohi ta hanyar ba su kudaden su kai tsaya daga asusun gwamnatin tarayya.

Gwamna Yari wanda ya samu wakilcin gwamnan jihar Bauchi M.A Abubakar, ya bada tabbacin gwamnoni za su yi aiki tare da Buhari don ganin sun aiwatar da tsarin a cikin ruwan sanyi. Da ya ke na shi jawabin, mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweremadu, ya ce akwai bukatar a karfafa kananan hukumomi tare da yi wa dokokin su garambawul.

Leave a Reply