Home Labaru Kiwon Lafiya Yanayi  Na Zafin : Cutar Ƙyanda Da Sankarau Na Yaduwa A Wasu...

Yanayi  Na Zafin : Cutar Ƙyanda Da Sankarau Na Yaduwa A Wasu Jihohin Najeriya

61
0

Masana lafiya a Najeriya na gargadi kan bazuwar cutar sankarau da ƙyanda a wasu sassan kasar nan, wadda ake alakantawa da yanayin zafin da ake ciki da ke kara ta’azzara lamarin.

Bayanai na cewa a wasu jihohin Najeriyar mutane da dama sun rasa rayukansu sanadiyar cutar sankarau, sakamakon bazuwar cutar wanda ke ɗarsa fargaba a zukatan al’ummar da cutukan suka bulla a yankunansu.

Jihohin Kano da Jigawa da Yobe na daga cikin wadanda aka bayyana cutukan sankarau da ƙyanda sun bulla.

Daraktan cibiyar binciken cutuka masu yaduwa a jami’ar Bayero da ke Kano Farfesa Isa sadiq Abubukar ya ce cutukan ba su da alaka da lokacin zafi, inda ya ce tun kafin lokacin ake kamuwa da cutar.

Ya ce alamun cutar sankarau na farawa ne daga zazzabi, da ciwon kai ka na wuyan mutum na kagewa yadda da ƙyar ya ke juyawa.

Leave a Reply