Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yan Ta’adda Sun Sace Manoma 55 A Neja

‘Yan bindiga sun fara tuntubar ‘yan’uwan akalla manoma 55 da su ka sace, yayin wasu hare-haren da su ka kai a gonakin su da ke kananan hukumomin Rafi da Shiroro a jihar Neja don neman biyan kudin fansa.

Wani mazaunin garin Pandogari, daya daga cikin garuruwan da ‘yan ta’addan su ka yi garkuwa da manoman ya tabbatar da halin da ake ciki.

Wata majiya ta ce, an samu nasarar karbo wasu daga hannun ‘yan bindigar bayan biyan kudin fansa, sannan akwai wasu mutanen da su ka samu kubuta daga hannun maharan a lokacin da su ke kokarin shigar da su daji.

A ranar Litinin da  ta gabata ne, gungun ‘yan ta’adda su ka afka wa yankin Allawa da ke karamar hukummar Shiroro, inda su ka kashe mutum  guda tare da sacce shanu sama da 100 da tsakar rana.

Bayanai sun ce baya ga tarin dabbobin, ‘yan ta’addan sun kuma yi awon gaba da manoma fiye da 55 yayin da su ke aiki a gonakin su, ciki kuwa har da mata da kananan yara.

Exit mobile version