Home Labaru ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hari A Garin Dapchi Da Ke Jihar Borno

‘Yan Ta’adda Sun Kai Hari A Garin Dapchi Da Ke Jihar Borno

450
0
‘Yan Ta’adda Sun Kai Hari A Garin Dapchi Da Ke Jihar Borno
‘Yan Ta’adda Sun Kai Hari A Garin Dapchi Da Ke Jihar Borno

Mayakan Boko Haram sun kai hari garin Dapchi da ke jihar borno, lamarin da ya tilastawa mazauna garin tsere zuwa cikin daji.

Wani mazaunin Dapchi ya shaidawa manema labarai cewa, ‘yan ta’addan sun isa garin ne a yammacin ranar Litinin, tare da yin harbin mai kan uwa da wabi, wamda hakan ya tsoratar da mutane suka fantsama cikin ndaji.

Haka kuma, mutumin ya kara da cewa, na hadu da mutane da dama a cikin dajin, inda a nan ne aka sanar da shi cewa, ‘yan ta’addan sun kone gidan hakimin garin.

Sai dai kafin maharan su kone gidan hakimin, sai da sun kwashe tufafin sa da kuma kayan abinci, inda daga bisani suka banka gidan fetur tare da cinna masa wuta.

Mutumin ya kara da cewa, lokacin da maharan suka isa gidan hakimin, bas u tarar da kowa ba, domin an gudu saboda harbi bindiga da suka ji ba kakkautawa.

A karshe ya ce, babu gawar ko mutum guda da ya ganin, sai dai sojojin sun shiga garin domin tabbatar da tsaro.