Home Home ’Yan Ta’adda Sun Fara Yaudarar Kananan Yara Zuwa Cikinsu

’Yan Ta’adda Sun Fara Yaudarar Kananan Yara Zuwa Cikinsu

100
0

Masu garkuwa da mutane sun dauki wani sabon salo na yaudarar kananan yara su shigo cikinsu a jihar Sakkwato.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya wasu masu garkuwa da mutane sun yaudari wasu kananan yara biyu a kauyen Baliyo da ke karamar hukumar Binji.

Wata majiya ta ce, kananan yaran na daga cikin mutane 15 da rundunar ’yan sandan jihar ta gabatar kan zargin yin garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Haka kuuma, rundunar ta zargin wasu mutane biyu da suka kasance iyayen gidan kananan yaran da laifin yin garkuwa da wasu mutane uku.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Ali Hayatu Kaigama ya ce bayan ’yan bindigar sun sace mutanen sun kai su wani wuri a cikin daji, sai suka gayyaci yaran biyu don yi masu gadin su.

Daya daga cikin kananan yaran ya shaida wa manema labarai cewa, suna kiwon dabbobi sai wasu mutane masu suna Jemmu da Usman suka zo a kan babur suka dauke su zuwa cikin daji, inda aka ajiye wasu mutane uku da aka sato, suka bukaci su lura da mutanen.

Leave a Reply